Tsaro
Rudunar ‘Yan Sanda ta bayar da umarnin bincike kan kisan Dadiyata

Rudunar ‘Yan Sandan kasar nan, ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan zargin da ke alakanta wasu manyan jami’an ‘yan sanda biyu da bacewar Abubakar Idris wadda akafi sani da Dadiyata.
Matakin ya biyo bayan wata takarda korafi da wani lauya mai zaman kansa a Kano, Abba A. Hikima, ya aikewa hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta kasa, inda ya bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin.
A wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta SolaceBase, lauyan ya bayyana cewa Sufeto Janar na ‘yan sandan ya tuntube shi da yammacin jiya Juma’a, tare da tabbatar masa da cewa za a gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen.
Hikima ya ce shugaban ‘yan sandan ya kuma sanar da shi cewa an dora wa wata tawaga ta musamman cikin rundunar alhakin gudanar da binciken.
An dai rasa Dadiyata tun watan Agustan shekarar 2019, lamarin da har yanzu ke ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce da tambayoyi daga sassa daban-daban na kasar nan.
Hikima ya ce idan har zarge-zargen karya ne, bincike zai wanke sunayen jami’an. Amma idan akwai gaskiya a ciki, dole ne a bari doka ta yi aikinta ba tare da la’akari da mukami ko iko ba.
You must be logged in to post a comment Login