Labarai
Rundunar Soji ta bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin samar da tsaro
Babban hafsan rundunar sojin kasa ta kasar nan Laftanal Janar Christopher Musa ya bai wa al’ummar Najeriya tabbacin cewa dakarun rundunar soji za su yi duk mai yiwuwa wajen dakile duk wata barazanar rashin tsaron dake faruwa a fadin kasar nan.
Laftanal Janar Christopher Musa, ya bayyana hakan ne a Talatar makon nan, lokacin da ya ke gabatar da jawabi ga dakarun Operation Hadarin Daji a jihar Sokoto.
Haka kuma, ya jinjina wa dakarun rundunar sojin kasa bisa irin namijin kokarin da suke yi na yaki da ayyukan ta’addanci a fadin Nijeriya musamman yadda suke nuna kwarewa a bakin aikin.
Ya kara da cewa rundunar tana sane da irin yadda dakarun nata suke rasa rayukansu da kuma yadda wasu suke samun munanan raunuka harma da irin yadda iyalansu suke jure rashinsu duka a yakin da suke yi da ayyukan ‘yan ta’adda a sassa daban – daban a Najeriya.
Laftanal Janar Christopher Musa, ya kuma bukaci dakarun da su yi hakuri kuma kada su gajiya, domin za su magance duk wasu matsalolin da kasar nan take fuskanta musamman yakin da suke yi da masu garkuwa da mutane da sauran ayyukan ‘yan ta’adda.
You must be logged in to post a comment Login