Manyan Labarai
Rundunar ‘yan sanda ta samar da tsaro don tunkarar zaben da za’a a Kano
Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta ce zata samar da ingantaccen tsaro a dukkannin kananan hukumomi tara da za’a sake gudanar da zabe a ranar 25 ga watan da muke ciki, domin ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.
Kwamishinan yansandan jihar Kano CP Habu Sani ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da Hukumar zabe ta kasa reshen Jihar kano ta shirya a yau Talata, a shirye shiryen sake gudanarda zabe a wasu daga cikin kananan hukumomin jihar Kano.
Habu A Sani ya kara da cewa rundunar ‘yansandan jihar Kano ta shirya tsaf domin ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da luma , kuma ba zata zuba idanu wasu mutane su tayarwa da jama’a hankali na a lokacin zabe.
Kano: mai amfani da kafafen sada zumunta ya zargi rundunar ‘yan sandan Kano da cin zarafinsa
Jigawa:Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane 7 a wani batsari da ya afku
Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta yi holin masu yin garkuwa da mutane
Wakilin Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa, hukumomin tsaro daban-daban ne suka halarci taro domin tabbatarwa da hukumar zabe ta Jihar kano shirin su na sake gudanar da zabe a wasu kananan hukumomin jihar Kano guda tara.