Labarai
Sama da mutane 10 sun rasa ransu sakamakon hatsarin mota a Kwara

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa (FRSC) ta ce mutum 10 sun rasa ransu a ranar Talata 20 ga watan Yuli a jihar Kwara sakamakon afkuwar wani mummunan hatsari mota.
Shugaban hukumar a jihar Jonathan Owoade ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya kuma ce, hatsarin ya afku ne a yankin Olooru-Okolowo a kan titin Ilorin-Jebba dake karamar hukumar Moro a jihar sakamakon gudun wuce sa’a da direban motar keyi.
Hukumar ta kuma ja kunnan direbobi da su guji gudun wuce sa’a a abubuwan hawa musamman a wannan lokaci da ake gudanar da bukukuwan sallah.
You must be logged in to post a comment Login