Labarai
Samar da ma’aikatar kula da dabbobi zai bunkasa tattalin arziki – kungiyar Miyetti Allah
Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da ma’aikatar da za ta rika kula da dabbobi a kasar nan wanda hakan zai basu damar bai wa kasar nan gudunmawa wajen farfado da tattalin arziki.
Sakataren kungiyar Alhaji Usman Ngelzarma ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a yau Alhamis.
Ya ce, a kasashen yammacin Afrika sun samar da irin wadannan ma’aikatu wanda hakan ya taimaka musu wajen magance matsalolin da suke fuskanta.
Alhaji Usman ya kara da cewa, bangaren da ke kula da su karkashin ma’aikatar aikin noma ba zai iya basu damar shiga wajen magance matsalar da kasar nan ke fuskanta ba, saboda haka yanzu lokaci yayi da Najeriya za ta amfana daga bangaren kiwo.
Gina Ruga ta zamani zai magance matsalolin Fulani -Munir Ahmad Gwarzo
Cin zarafin Fulani makiyaya babu abinda zai janyo sai kara rura wutar rikici- Hassan Kukah
Shugaba Buhari ya ce ‘yan Najeriya su yi watsi da kiran dattawan Arewa kan dawowar Fulani
Cikin matsalolin da ya lissafo ya ce suna fuskantar satar dabbobi da yin garkuwa da mutane da rikicin makiyaya wanda ya sanya har yanzu basa samun damar kula da rumbunan adana kayayyakin su.
You must be logged in to post a comment Login