Labarai
Sarkin Katsina na Shirin korar Shirin AGILE daga jihar
Mai Martaba Sarkin Katsina, Abdulmuminu Kabir, na shirin korar shirin nan na inganta ilmin ’yan mata mai suna AGILE daga fadin jihar.
Sarkin ya ce, shirin na AGILE yana wuce gona da iri da kuma kokarin gurbata tarbiyyar Musulunci da ta al’ada da aka san yankin da ita.
Sarkin ya bayyana haka ne a fadarsa ranar Asabar lokacin da yake aiwatar da wasu nade-nade.
Kazalika, ya ce shirin yana cin karo da koyarwar addinin Musulunci wanda ya ce a matsayinsu na iyayen al’umma ba za su bari hakan ta faru ba.
Don haka ya ce, lallai ne wannan shiri ya fita daga Jihar Katsina baki daya.
Shiri AGILE na da nufin habaka ilmin zamani na ’yan mata daga karamar makaratun sakandaren zuwa babba, inda ma har ake ba su wani ihisani.
Sai dai wasu masu nazari da suka yi sharhi a kai sun ce shirin in baya ga bata tarbiyya da kokarin sanya daliban bujire wa iyaye da wasu ka’idodi da tarbiyar addini da ta al’ada babu abin da shirin yake koyarwa.
You must be logged in to post a comment Login