Labarai
Sarkin musulmi yayi kira ga shugaba Buhari ya kawo karshen matsalar kudin da ake fama dashi a kasar nan
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya bukaci shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari da ya dauki matakan gaggawa na shawo kan wahalar da jama’a ke ciki a sanadiyyar sauyin kudi domin kaucewa bore.
Sarkin Musalmin ya nuna takaicinsa kan lamarin tare da nuna damuwa musamman yadda jama’a suka fada cikin yanayi na yunwa da bacin rai saboda sauyin kudin.
Wannan dai na zuwa ne yayin da ya rage kwana guda wa’adin da kotun Kolin kasar nan ta bayar na hana Babban bankin kasa aiwatar da tsarinsa na daina amfani da tsofaffin kudin a ranar 10 ga watan nan na Fabarairu.
A gobe laraba ne dai kotun kolin za ta yanke hukunci kan karar da gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar a kan harkokin kudi.
You must be logged in to post a comment Login