Labarai
Satar dalibai – An haramta yin kabu-kabu a jihar Neja
Gwamnan jihar Neja, Sani Bello ya sanya dokar hana kabu-kabu a Minna babban birnin jihar daga ranar Alhamis 3 ga watan Yuni.
Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin mataimakinsa Ahmed Mohahammed ketso.
Ya ce, daga ranar Laraba ababen hawa na gida za su rika zirga-zirga a tsakanin karfe 6 na safe zuwa 9 na dare a kowace rana.
“Muna sa ne da cewa masu garkuwa da Mutanen na amfani da baburan kabu-kabu wajen siyo kayan masarufin da suke amfani da su” inji Ketso.
A cewar sa umarnin na a matsayin wani mataki na ganin an sako daliban makarantar Islamiyya na Tegina da aka sace.
You must be logged in to post a comment Login