Labarai
Saukar Alkur’ani : Sarkin Kano ya ja kunnen Iyaye
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce, iyaye sai sun ƙara kula da ilimin Islamiyyar ƴaƴan su wajen biyan kuɗin makaranta domin su samu tarbiyyar da za a yi alfahari da su a nan gaba.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne a yayin saukar Alkur’ani mai girma na makarantar Tagrisu Hubbin Nabiyyi (S.A.W) Lil-hayatil Islamiyya dake unguwar Tukuntawa a ranar Laraba.
Ya ce, ya zama wajibi iyaye su kula da ilimi da tarbiyyar ‘ƴa’ƴan su ta hanyar bibiyar karatunsu na Islamiyya domin sauke nauyin dake kan su.
Sarkin ya kuma ce, malamai suma sai sun riƙe amanar da iyaye su ka basu na ilimantar da ‘ƴa’ƴan su domin samun ilimin da su zama manyan gobe nagari.
A nasa ɓangaren, Dagacin Gandun Albasa, Alhaji Ƙasim Yakubu, jan hankalin ɗaliban ya yi da su amfana da ilimin da suka koya wajen yin biyayya ga iyayensu da kuma shugabanni.
Sarkin Kano Aminu Ado Bayero shi ne shugaban majalisar sarakuna – Ganduje
Abubuwan da suka faru a Katagum yayin ziyarar Sarkin Kano
Masu magungunan dabbobi su rinka hada kai da masana – Sarkin Kano
Sarkin Zazzau ya fashe da kuka ya yin nadin sa a Zariya
A nasa jawabin, Uban makaranta, Dr. Faruk Ahmad Kurawa, ya buƙaci gwamnati da masu kuɗi da su tallafawa makarantar domin samun wurin karatu na din-din-din.
Wakilin mu Buhari Isah ya rawaito cewar, a yayin saukar Alkur’anin na ɗalibai 34 karo 2 an karrama masu baiwa makarantar gudunmawa da suka haɗa da, Dagacin Gandun Albasa Alhaji Ƙasim Yakub da Dr. Faruk Ahmad Kurawa da kuma Farfesa Rabi Muhammad Hashim.
You must be logged in to post a comment Login