Labarai
Saura ƙiris a sako ɗaliban Kagara – Dr. Gumi
Fitaccen malamin addinin Islaman nan Dr. Ahmad Mahmud Gumi ya ce nan ba da daɗewa ba za a sako ɗaliban makarantar Kagara da ƴan bindiga suka sace.
Dr. Gumi ya shiga dajin Kontonkoro domin tattaunawa da ƴan bindigar kan sakin ɗaliban.
Gumi ya ce, tuni ya tattauna da shugabannin ƴan bindigar kan batun satar ɗaliban.
Wasu bayanai sun nuna cewa, tuni gwamnatin jihar Neja da takwararta ta Zamfara suka duƙufa wajen ceto ɗaliban.
Wani shaidar gani da ido ya shaidawa manema labarai cewa jami’an gwamnatin jihar Neja da na Zamfara sun shiga dajin Kotonkoro da ke Dutsin Magaji don tattauna yadda za a sako ɗaliban.
A ranar Laraba ne ƴan bindigar suka kutsa kai makarantar Sakandiren kimiyya ta Kagara da ke jihar Nejan inda suka hallaka guda sannan suka yi awon gaba ɗalibai sama da 40.
You must be logged in to post a comment Login