Labarai
Shan Zakami ya haifar da asarar rayuka a Katsina
Rundunar ‘yan sanda jihar Katsina ta cafke wasu matasa biyu da take zargi da sanya Zakami acikin abincin gidan biki, wanda yayi sanadiyyar rasa rayuka.
Wannan al’amari dai ya faru ne a kauyen Ali Yaba dake karamar hukumar Mani, inda wani matashi mai suna Musa Sulaiman dan shekareu 25 ya baiwa wata matashiya mai suna Shafa’atu Surajo ‘yar shekara 20 aikin yin girkin gidan biki, wanda aciki aka sanya Zakami aciki.
Hakanne kuma ya haifar da sanadiyyar mutuwar mutane biyu daga cikin ‘yan biki, yayin da wasu kuma da dama suka jikkata.
Shafa’atu Surajo da ake zargi da aikata wannan danyen aiki ta ce ita ba ta san menene ba, kawai ya bata aiki sannan ya kawo mata ruwa a jarka cewa ta zuba acikin abincin da za ta dafa.
Shi ma a nasa bangaren Musa Sulaiman cewa yayi hakan ne, domin shi da abokanan sa su sha, ba don sauran al’umma ba.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina SP. Isah Gamo ya ce yanzu haka suna rike da wannan matasa, inda suka cigaba da bincike akai.
Karin labari:
Rundunar ‘yan sandan Katsina ta kwato Shanu sittin
Za’a fara rataye masu garkuwa da mutane a Katsina
Ku kalli tattaunawa da wadanda ake zargin cikin bidiyo:
You must be logged in to post a comment Login