Labaran Wasanni
Shekaru 25 rabon da Afrika ta Kudu ta lashe kofin Afrika
A makamanciyar irin wannan ranar ce ta uku ga watan Fabrairun shekarar 1996 kasar Afrika ta Kudu ta kafa tarihin lashe gasar cin kofin kasashen nahiyar Afrika karo na farko.
Shekaru ashirin da biyar ke nan da suka gabata da Bafana Bafana suka taba daukar kofin na nahiyar Afrika a tarihin kwallon kafar kasar duk da kasancewarta cikin manyan kasashe a nahiyar ta Afrika.
Kwararran masani a fannin wasan kwallon kafa a kasar Mark Gleeson ya ce wannan rana ta zamo abar kwatance ga kasar sai dai tun daga wance lokacin zuwa yanzu kasar ta gaza maimaita irin wannan tarihin.
Afrika ta kudu dai ta doke Tunisia da ci biyu da nema a wasan karshe a gasar ta cin kofin Afrika da aka fafata a shekarar ta 1996 a filin wasa na Soccer City dake a Afrikan ta kudu.
You must be logged in to post a comment Login