Labaran Wasanni
Shin kokun san wanene Abdul Attacker
Bayan taka Leda a wasu kananan kungiyoyi na cikin unguwa a yankin kofar waika da kewaye.
Daga bisani kungiyar Golden bullet ta gano irin baiwar da Allah ya yi masa a kwallon kafa kuma nan take ta daukoshi kuma ta soma gwadashi cikin matasan yan wasan ta.
Cikin kankanin lokacin Abdul attacker ya tsere wa tsararsa abunda yasa duk da karancin shekarun sa ta maida shi Dan wasan ta na gaba a babbar tawagar ta.
Shekaru kalilan ya kwashe a kungiyar amma ficen dayayi wajen cin kwallo a raga ta kowane hali yasa kungiyoyin kwallon kafa a jihar Kano suka soma maida hankali akan sa, inda kungiyar Dabo bebies ta samu nasarar daukeshi a shekarar 2017.
Alokacin ne kuma mahukuntan kungiyar suka yanke shawarar mai dashi jerin manyan yan wasan ta masu jefa mata kwallo, hakan kuwa ya biyo bayan tafiyar Fitaccen lamba taranta Nazifi Yahaya.
Victor Osimhen bazai buga wasanni biyu ba a gasar Seria A
Mikel Arteta ka iya rasa aikin sa idan Arsenal ta yi rashin nasara a wasanni uku masu zuwa
Tun daga wannan lokacine Abdul attacker ya zamo gagara badau a fannin jefa kwallo a raga.
A shekaru uku da rabi a kungiyar Dabo bebies Abdul attacker ya jefa kwallo 55 a raga inda ya temaka aka jefa sama da 30.
Cikin kungiyoyin da ya azabtar dai harda Kano Pillars da ya jefawa kwallo biyu awani wasan sada zuminci da su ka yi a shekarar 2021.
Ya dai jagoranci Dabo bebies wajen daga kofuna sama da 20. Ciki harda gasar Tofa Premiere. Wadda ashekarar ne ma ya lashe golden boot wato kyautar Dan wasan dayafi jefa kwallo a raga.
Dan shekaru 19 yanxu haka dai kungiyoyin gasar Firimiyar Najeriya da damane suka nuna sha’awar daukan dan wasan.
You must be logged in to post a comment Login