Siyasa
Shugabannin Labour Party na jihohin kasar sun jaddada goyon baya ga Julius Abure
Shugabannin jam’iyyar adawa ta Labor Party na jihohin sun jaddada goyon bayansu ga shugaban jam’iyyar Julius Abure da umurnin kotu ta dakatar a baya.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC Komred Joe Ajero, ya fitar mai dauke da sa hannun sa kungiyar wadda ita ce ke da mallakin jam’iyyar ta LP, ta ce, Abure ta sani a matsayin shugaba.
Tun biyo bayan umurnin kotu na dakatar da Abure, magoya baya da dama sun yi ta yin dafifi a shalkwatar jam’iyyar domin hana shi yin jagoranci.
Sai dai Shugabannin jihohin sun ce wadanda su ke adawa da Abure na halin dakatarwa ne kafin su dau matakin don haka ba su da hurumin yin hakan.
Shugabannin sun kara da cewa, ya kamata kowa ya jira har sai an kammla shari’a kafin kawo kowane korafi.
You must be logged in to post a comment Login