Labarai
Silas Nwanko ya zama gwarzon dan wasan NPFL na 2021

Dan wasan gaba na tawagar Nassarawa United ,Silas Nwanko ya zama gwarzon dan wasan gasar Firimiyar Najeriya ta bana 2020/21,da aka kammala a wani taro da Kamfanin shirya gasar LMC, da hukumar Kwallon Najeriya NFF, suka shirya .
Taron ya gudana a Otal din Eko dake jihar Lagos, inda dan wasan ya samu kyautar zama dan wasa mafi hazaka na bana a gasar.
“Naji dadin karrama ni da akayi inda hakan ke nuni da cewar akwai ‘yan wasa hazikai a gasar Najeriya”.
” Kungiyata ta Nassarawa United Babbar tawaga ce , Ina godewa Allah da al’ummar jihar Nassarawa da abokanan Kwallo na ” inji dan wasa Silas Nwanko , a zantawar sa da manema labarai Jim kadan Bayan kammala zaben shi.
Tsohon dan wasan Sunshine Stars , Nwanko ya zura kwallaye 19, da yayi kan kan kan da dan wasan Akwa United, Charles Atshimene ,a yawan kwallaye.
You must be logged in to post a comment Login