Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Siyasar Kano: Ko Baffa Bichi ya ƙwace takarar Abba Gida-Gida?

Published

on

Alaƙa tsakanin Kwankwaso da Baffa Bichi
Bayanai sun nuna akwai tsohuwar alaƙa tsakanin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da Dr. Abdullahi Baffa Bichi amma ta ƙara ƙarfi a lokacin zaɓen 2019.

Wani makusancin Dr Bichi ya ce, tun a zaɓen 2011 Baffan ya rungumi tafiyar Kwankwasiyya a sirrance.

Ya ce, “A 2018 bayan da tsohon mataimakin gwamna Hafizu Abubakar ya fice daga APC ya dawo PDP, wata jami’a ta bashi digirin girmamawa a Amurka”.

A lokacin Kwankwaso da Hafizu da kuma Baffa Bichi tare suka tafi Amurka don ƙarɓar girmamawar a cewar makusancin na sa.

Cikin Hoto: Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, Dakta Abdullahi Baffa Bichi da Injiya Abba Kabir Yusuf.

Baffa Bichi da tafiyar Kwankwasiyya
A zaɓen 2019 dai Baffa Bichi na cikin waɗanda suka bada gudunmawa ga ɓangaren Kwankwasiyya duk da cewar yana jam’iyyar APC.

Ko Baffa Bichi ya bar jam’iyyar APC?
Har yanzu Baffa Bichi bai sanar da cewa ya fice daga APC ba.
Sannan bai sanar cewa ya koma jam’iyyar PDP ba.

Ƙungiyar One to tell ten da Kwankwasiyya
Yanzu haka dai dukkan ofisoshin ƙungiyar ta 1 to tell 10 da Baffa Bichi ke jagoranta a jihohi 19 na Arewa, sun rikiɗe sun koma Kwankwasiyya, haka ma magoya bayan ta.

Baffa Bichi ba ya sa jar hula
Har kawo wannan lokaci dai Bichi bai fara sanya jar hula ba, wadda ta ke cikin manyan alamu na mabiya Kwankwasiyya.
Sai dai da yawan mabiyansa tuni suka rungumi tsarin sanya jar tagiyar.

Dakta Abdullahi Baffa Bichi da Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso a cikin jirgi.

Tafiye-tafiyen Kwankwaso tare da Baffa Bichi
Sannu a hankali yau da gobe na nuna cewa Baffan yana tare da Kwankwasiyya.

La’akari da yadda ya ke bin tawagar tsohon gwamna Kwankwaso.

Hotunan Kwankwaso da Baffa Bichi sun karaɗe kafafen sada zumunta a wuraren taruka mabanbanta.

Ku kalli wasu hotunan Kwankwaso da Baffa Bichi a ƙasa

Ko Baffa Bichi ya ƙwace takarar Abba Gida-Gida?
Wasu daga tsagin jam’iya mai mulki tuni suka fara zargin cewa, da alama Baffan ya yi awon gaba da takarar Abba K. Yusuf.

Alal misali, tsohon kwamishinan gwamnatin Kano Mu’azu Magaji Ɗan Sarauniya.

Mai bai wa gwamnan Kano shawara Fa’izu Alfindiki sun sha wallafa bayanai a kafafen sada zumunta kan cewa yanzu takarar PDP alamu na nuna ta koma hannun Baffa Bichi.

Masu wannan iƙrari dai na kafa hujja da hotunan da kuka gani a sama na yawace-yawacen da Kwankwaso ke yi da Baffa Bichin.

Inda wasu ke cewa, yadda ake ganinsa da Bichi a yanzu har ya zarce yadda ake ganinsa da Abba Gida-Gida a baya.

Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da Dakta Abdullahi Baffa Bichi.

Me Abba Gida-Gida ya ce game da hakan?
Abba Kabir ya yi martani a kai, ta cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa Malam Ibrahim Adam.

Sanarwar ta ce, zargin cewa Kwankwaso ya maye gurbin takarar Abba Gida-Gida zance ne mara tushe.

“Ba zaɓen 2023 ne a gaba na ba, saboda mulki na Allah ne, abin da muka sa a gaba yanzu shi ne ci gaba da haɗin kan tafiyarmu ta Kwankwasiyya” inji Abba.

Yanzu dai za a iya cewa kallo ya koma sama domin ganin ko yaya za ta kasance a shekarar 2023.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!