Labarai
Sojoji sun gargaɗi masu katsalandan kan matsalar tsaro
Rundunar sojin kasar nan ta ce lokaci ya yi da ƙasashen duniya za su daina nuna mata yatsa game da yadda ta ke gudanar da ayyukanta na samar da tsaro.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar sojin Kanal Sagir Musa ne ya bayyana haka a wata sanarwar bayan taro da ya fitar jiya Litinin a Abuja.
Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da matsalar rashin tsaron ke ci gaba da ta’azzara a wasu yankunan ƙasar nan.
Cikin sanarwar rundunar sojin ta lashi takobin ci gaba da gudanar da aikinta na tabbatar da tsaro da hadin kan Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login