Addini
Tahajjud: ba za mu yarda a fake da ibada a rika sabon Allah ba – Ibn Sina
Hukumar Hisba ta jihar Kano ta gargadi matasa masu fita sallar Tahajjudi da su guji aikata ayyukan da ya sabawa ka’idojin addinin musulunci a yayin fita sallar.
Shugaban hukumar Sheikh Harun Mahammad Sani Ibn Sina ne ya sanar da hakan ta cikin wani sakon murya da ya aikowa Freedom Radio.
“Mun baza jam’an mu a dukkanin kananan hukumomi 44 na Kano, domin su sanya ido kan yadda ake karakainar zuwa sallar, don tabbatar da an bi dokoki”.
“Wasu bata gari na jan yan mata gefe su kafa dandalin hira yayin da suka fito sallar, to wannan dabi’ar ba za mu yarda da ita ba, kuma jami’an mu za su tabbatar ba samu masu yin ta ba” a cewar Ibn Sina.
Muhammad Harun Ibn Sina ya kuma ce, sun bai wa jami’an su umarnin su sanya ido kan ababen hawan masallata domin dakile ayyukan bata gari, kuma matukar aka kama wadanda suka karya doka to kuwa za su fuskanci hukunci.
You must be logged in to post a comment Login