Labarai
Tattalin arzikin Najeriya na gab da durkushewa -Muhammadu Sanusi Na II
Tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN), Malam Muhammadu Sanusi, na II, ya ce tattalin arzikin Najeriya na gab da durkushewa.
Muhammadu Sunusi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen rufe babban taron zuba jari na jihar Kaduna a ranar Juma’a 24 ga watan Satumbar shekarar 2021.
Tsohon gwamnann bankin kuma tsohon sarkin Kano ya ce kasar nan na fama da kalubale wajen hakar man fetur, a cewar sa ya zama wajibi a mayar da hankali wajen inganta tattalin arzikin kasar.
Ya kuma ce nan bada dadewa ba za’a iya rasa sinadarin dake bayar da Zinare a kasar nan, idan har ba’a mayar da hankali wajen inganta bangaren ba.
Muhammadu Sanusi ya ce, yayin da kasar Ghana dake da karancin tattalin arzikin kasa, ke saka kudade masu yawa a bangaren ilimi, ita kuwa Najeriya na saka kashi 7 cikin 100 kawai a bangaren.
You must be logged in to post a comment Login