Manyan Labarai
Tsarin albashi na IPPIS: Kungiyar Malaman Jamioi na Jayayya da Gwamnatin tarayya.
Tun ranar takwas ga watan Oktoban da muke ciki ne shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin da yake gabatar da kasafin kudi na shekarar 2020 yace daga ranar 31 ga watan Oktoba kowanne ma’aikacin gwamnatin tarayya sai ya shiga tsarin nan na biyan albashi da ake kira da IPPS.
Shugaba Buhari yayi wannan jawabi sakamakon yadda ake ganin cewa tsarin na IPPS mataki ne da gwamnatin tarayya take da shi na biyan albashin maaikatan ta ba tare da wata matsala ko kadan ba da ta hada da magance cin hanci da rashawa.
A da, wasu ma’aikatu ne dai na gwamnatin tarayya ake biya albashi ta tsarin bai daya da ake wa lakabi da IPPIS, inda wasu bangarori suka dade suna kokawa akan haka, musamman ma bangaren jami’an tsaro da suka hada da sojoji da hukumar ‘’yansanda da hukumar gyara halaye ta Najeriya wato NCS da sauran gurare.
Wasu bangarorin na Gwamnatin tarayya musamman bangaren jami’an tsaro sun koka da yadda suke samun albashin su kafin a saka su a tsarin na IPPIS ,har sai da gwamnatin tarayya ta saka hukumomin tsaron a tsarin na IPPIS, sannan su ka samu sauki wajen karbar albashin nasu .
A makwannin nan da muke ciki kungiyar malaman jami’oi ta kasa wato ASUU ta ja daga da gwamnatin tarayya na cewa su ba zaa saka malaman jami’a a tsarin na IPPIS ba.
Wannan dambarwa dake faruwa tsakanin Gwamnatin ta tarayyar Najeriya da malaman jamio’in kasar nan na neman barin baya da kura, inda ita gwamnatin tarayyar ta Najeriya ta ja daga, inda tace lallai sai kowanne ma’aikacin gwamnatin ta tarayyar Najeriya ya shiga tsarin na biyan albashi ta IPPIS.
A satin nan da muke ciki ne dai kungiyar Malaman jamio’in ta Najeriya ta rika tattaunawa da sauran jami’an gwamnatin tarayya a game da hanyar biyan albashin na bai daya wato IPPIS amma samun matsaya yaci tura har yanzu.
Bayanai da ke fitowa na nuni da cewa kungiyar ta ASUU na shirin fadawa yajin aiki muddin Gwamnatin tarayya ta dage a saka su a tsarin biyan albashin na IPPIS ,ita ma kuma gwamnatin tarayya ta cigaba da kafewar cewa babu gudu babu ja da baya a game da saka kowacce ma’aikatar gwamnatin tarayya a tsari na biyan albashi na IPPIS.
Ko a kwanannan ma , sai da ministar kudi Hajiya Zainab Ahmad tace saka Malaman jamia a tsarin na IPPIS umarni ne na shugaba Muhammadu Buhari.
A kwai dai bayanai dake nuna cewa malaman jamiar ta Najeriya na koyarwa a jamio’i da dama ,bayan jamio’in su na asali, hakan ta sa ake ganin saka malaman jamiar a tsarin na IPPIS abune da zai hana su karbar albashi da yawa a maimakon albashin su na asali.