Labaran Wasanni
Tsohon Kocin Atletico Madrid ya mutu
Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid da Barcelona da Real Madrid, Radomir Antic, ya mutu hakan ya biyo bayan rasuwar mahaifiyar mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Joseph Gurdiola wadda ita ma ta rasu a jiya bayan fama da cutar Corona.
Radomir Antic ya rasu yana da shekaru 71, bayan gajeruwar rashin lafiya da bata da alaka da cutar Corona, wadda ake fama da ita a halin yanzu a fadin duniya.
Antic wanda ya shafe shekaru 27, yana horar da kungiyoyi daban -daban ya yi kaurin suna ne a kungiyar Atletico Madrid, wacce ya jagoranta wajen lashe gasar LA liga, da kofin kalubale a kasar wato Copa Del Rey a shekarar 1995-96, kafin daga bisani ya rike kungiyoyin Barcelona da Real Madrid.
Labarai masu alaka.
Yanzu-yanzu: Dan wasan kungiyar Enugu Rangers ya Mutu
Muller ya saka hannu a sabon kwantiragi da Bayern Munich
Tuni dai shugaban kungiyar Atletico Madrid, Miguel Angel Gil, ya nuna alhinin sa tare da mika ta’aziyyar sa ga iyalin mamacin tare da cewar an yi rashin gwarzon hazikin jagora, in da kungiyoyin Madrid da Barcelona, suma suka aike da sakon ta’aziyyar su.
Radomir Antic, dan kasar Serbia, ya rike kungiyoyi da dama ciki har da kasar sa ta haihuwa, da suka hada da , Real Zaragoza, Celta Vigo, Real Oviedo, kafin ya karbi aiki a Barcelona a shekarar 2003 da ya canji Luis Van Gaal, ya karkare a kungiyar Hebei China Fortune, a kasar China,a shekarar 2015.
You must be logged in to post a comment Login