Labarai
Wani bazawari ya fito da hanyar karbar waya a hannun mata
Shi dai wannan mutum ya kasance yana karbar waya ne a hannu zauarawa da “yan mata ne da sunan soyayya a unguwar yakasai cikin birnin Kano.
Asirin mutumin ya tonu ne a lokacin da ya karbi wayar wani baiwan Allah da sunan zai dan saka layin sa yayi waya bayan kuma ya karbi wayar sai ya gudu da ita ba’a kara ganin sa ba sai bayan wasu ‘yan kwanaki inda shi kuma yace bazeyadda ba sai ya biya shi dalilin da yasa hakan takai da zuwa ofishin ‘yansanda da yake kwalli.
Bincike da ‘yansanda sukayi ya tabbatar da cewa shi daman wannan mutun halinsa kenan domin kuwa bai tsaya a kan Mata ba harma da Maza don kuwa har Kaninsa yayi wa haka.
‘Yan sanda sun kama mai damfarar matasa
‘Yan yahoo sun damfari loba boy
Hukumar EFCC ta cafke masu kamfanin boge da bindigu a Kano
Tuni dai aka gabatar da wannan matashi a gaban kotun shari’ar Musulunci dake cikin Jihar Kano mai lamba 2 inda shi kuma ya musanta faruwar lamari.
Mai shari’a ya bada umarnin da a cigaba da tsare shi wannan mutun har zuwa lokacin da za’a cigaba da Shari’a.