Manyan Labarai
Wasu ministoci sun kamu da Corona a Afrika Ta Kudu
Gwamnatin Afrika ta kudu a yau talata ta sanar da cewa ministocin ta biyu sun kamu da cutar corona .
Ministocin wadanda a jiya litinin rahotanni suka bayyana cewa sun kamu da cutar bayan yi musu gwaji da ya hadar da ministan kwadago Thulas Nxesi mai shekarau 61 sai ministan albarkatun kasa Gwede Mantashe mai shekaru 65 wanda kuma tuni aka killace su a asibitin kula da masu fama da cutar.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar zartaswar kasar Phumla Williams ya fitar a jiya litinin.
Sanarwar ta bayyana cewa tuni jami’an lafiya suka bada umarnin killace su don basu kulawar da ta dace daga jami’an lafiya.
Ta cikin sanarwar dai, Thulas Nxesi yace tun a baya akwai ministoci uku da suka taba kamuwa da cutar a Afrika ta kudu wadda kuma ita ce kasa da take da mafi yawan masu dauke da cutar a Afrika ta kudu kuma it ace kasa da take mataki na biyar a duniya baya ga kasashen Brazil da India da kuma Russia.
Cikin ministocin da suka taba kamuwa dai akwai ministan tsaron kasar Nosiviwe Mapisa-Nqakula wanda kuma ya warke a ranar juma’ar da ta gabata kamar yadda gwamantain kasar ta bayyana.
A yanzu haka dai kasar Afrika Kudu Afrika ta fitar da rahoton cewa adadin masu dauke da cutar corona a kasar sun kai 373,628 yayin da guda 5,173 suka rasa rayukan su sanadiyyar cutar.
You must be logged in to post a comment Login