Labarai
Wata kotu a Kano ta yanke hukuncin kisa ga wani matashi
Wata babbar kotun shari’ar musulnci dake zaman ta a Kano karkashin mai shari’ah Aliyu Muhammad Kani, ta yake hukuncin kisa ga wani matashi Yahaya Sharif Aminu Sharifai, bisa samun sa da laifin aikata batanci ga fiyayyen halitta manzo sallalahu alaihi wasallama, ta hanyar rubutu a wani group din WhatsApp.
Ka zalika wani matashi Umar Faruk Bashir dan unguwar Sharada, da shima kotun ta yankewa hukuncin shekaru goma tare da aiki mai tsanani a gidan ajiya da gyaran hali, sakamakon samun sa da kotun ta yi da laifin aikata sabo ga Allah subahahu wata’ala, ta hanyar yin musu a majalisa.
Tun a baya dai dan sanda mai gabatar da kara a kotun Aminu Sani ‘Yar Goje, ya karanta musu kunshin tuhumar sun kuma amsa.
Wakilin mu Abubakar Sabo ya ruwaito cewa, bayan an yanke hukuncin an danka masu laifin a hannun jami’in gidan ajiya da gyaran hali, Yakubu Bala Jibrin bisa jagorancin mai magana da yawun su DSC Musbahu Lawan Kofar Mata.
You must be logged in to post a comment Login