Kiwon Lafiya
WHO ta amince a fara amfani da rigakafin allurar zazzabin Maleria
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta amince da fara amfani da nau’in allurar rigakafin zazzabin cizon sauro na Malaria, nau’in allurar da ke matsayin irinsa na farko da hukumar ta amince da amfani da shi kan jama’a don yaki da cutar.
A jiya Laraba 06 ga watan Oktobar 2021 ne WHO ta amince da rigakafin da wani kamfani mai suna GlaxoSmithKline ya samar.
Cutar zazzabin cizon sauro ta Malaria dai na kashe akalla mutanae Miliyon 500 a duk shekara a yankin Afrika kadai da mafi akasarin su yara ne kanana.
Matakin na WHO na zuwa bayan gwajin alluran rigakafin na Malaria ko kuma zazzabin cizon sauro har fiye da miliyan 2 a kasashen Ghana Kenya da kuma Malawi cikin shekarar 2019.
Sanarwar da WHO ta fitar ta ruwaito Pedro Alonso daraktan shirin yaki da Malaria na hukumar na cewa matakin babban ci gaba ne a yaki da cutar da kan kashe yaro guda duk bayan mintuna biyu.
Cutar ta Malaria da sauro ke yadawa na jerin cutuka mafiya kisa yanzu haka a Duniya, inda tafi kamari a kasashen Afrika da gabashin nahiyar Asiya.
You must be logged in to post a comment Login