Kaduna
Yan arewa ba za su sake zabar shugaba wai kawai don shi dan arewa ne.
Shugaban kungiyar dattawan arewa ta (Northern Elders Forum) farfesa Ango Abdullahi, ya ce, al’ummar arewa sun koyi darasi mai daci, saboda haka ba za su zabi shugaban kasa a shekarar 2023 bisa la’akari da addinin-sa ko kabilar-sa ba.
A cewar Ango Abdullahi, al’ummar arewa sun koyi darasi mai ciwo da ba za su manta da shi da sauki ba.
Farfesa Ango Abdullahi wanda tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zari’a, ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke jawabi a garin Kaduna, yayin taron da kungiyar dattijan arewa ta shirya.
Ango Abdullahi ya fito karara ya gargadi ‘yan siyasar arewa da su shiga taitayinsu domin yanzu ba su da wani tabbaci na cewa al’ummar arewa za su kada musu kuri’a kawai saboda gadarar cewa su ‘yan arewa ne.
Shugaban kungiyar ta NEF wanda mai magana da yawun kungiyar Dr. Hakeem Baba Ahmed ya wakilta, ya ce, ‘yan arewa sun koyi darasi saboda haka duk wani bazauri da ya fito yana zawarcin kuri’unsu a shekarar 2023 sai sun yi mishi kallo na tsanaki tare da nazartar manufofin-sa kan yankin arewa da ma kasa baki daya.
‘‘Kar wani dan arewa ya zaci cewa ‘yan arewa za su kada masa kuri’a a zaben shekarar 2023 saboda kawai yana gadarar shi dan arewa ne’’
‘‘Arewa sai ta kalli duk wani dan takara, ta tantance-shi, ta tsefe-shi tas, ta tabbatar da nagartar-sa/ta kafin ta amince maka/mata’’ a cewar Ango Abdullahi.
You must be logged in to post a comment Login