Labarai
‘Yan sanda a Kano sun gargadi jama’a kan aikata laifi ranar bikin Maukibi
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano gargadi al’umma, musamman bata gari da suke fakewa da lokacin taron jama’a domin aikata laifukan sara suka, da sauransu.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya rabawa manema labarai a daren yau, ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ta shirya tsaf domin kula da shige da fice aranar Asabar mai zuwa da za’a gudanar da bikin maukibin waliyai da mabiya darikar Qadiriyya gabatarwa duk shekara a Kano.
DSP. Kiyawa ya bayyana cewa sunyi shiri na musamman domin zakulo wadanda suke fakewa da irin wadannan taruka su tayar da hankalin jama’a, a don haka suna gargadin al’umma dasu guji yin shigar banza, ko sanya kayan mata ko kuma yin wata shiga wadda ta saba da al’ada ko kuma addinin al’ummar jihar Kano.
Labarai masu alaka:
Rundunar ‘yan sandar jihar Kano ta sake ceto wani yaro a Anambra
Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta yi holin masu yin garkuwa da mutane
Kazalika rundunar ‘yan sandan jihar Kano tayi shiri na musamman domin dakile masu ta’ammali da miyagun kwayoyi, da sara suka ko kwacen wayoyi da sauran laifuka a yayin gudanar da taron maukibi na bana.
Haka kuma rundunar ‘yan sandan jihar Kano na sanar da jama’a cewa har yanzu dokar nan tana nan ta haramta yin wani gangami ko zanga-zanga ko wani taron jama’a ba bisa ka’ida ba, kuma duk wanda ya karya wannan doka to babu shakka hukuma zatayi aiki akansa a cewar, kuma anyi hakan ne domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano a cewar DSP. Kiyawa.
A karshe rundunar ‘yan sandan ta taya al’ummar musulmi murnar zagayowar wannan wata da fatan za’a kammala bukukuwa lafiya.
Labarai masu alaka:
‘Yan film sun karrama kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano