Labarai
Yan sanda sun kama wasu matasa dayin dafara a Kano
- Rundunar ‘yan Sandan ta kama matasan biyu ne da shaidar wani gidan radiyo na bogi a nan Kano.
- Wadannan matasan har ila yau tana zargin matasan da yin dafara .
- Yanzu dai matasan na hannun Rundunar domin gudanar da bincike.
Rundunar ‘yan sandan a Jihar Kano ta samu nasarar kama wasu ‘yan Jarida na bogi suna damfarar mutane ta hanyar tura musu sakon karta kwana na karya.
Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ya bayyana hakan.
SP Kiyawa yace sun kama matasan su biyu da ake zargi dauke da katin shaidar wani gidan Radio mai zaman kansa a nan Kano lokacin da suka je wani shagon siyarda kaya suka tura musu Alert na karya
Matasan biyu da ake zarginsu suna damfarar mutane masu suna Mujahid Muhammad da kuma Abba Imam sun amsa zargin da ake musu.
Freedom Radio ta ruwaito cewa rundunar ta ce ‘da zarar ta kammala bincike akan wadanda ake zargin nasu, zata gurfanar dasu a gaban kotu domin su girbi abinda suka shuka.
Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa
You must be logged in to post a comment Login