Labarai
‘Yan sanda sun yi holen wadanda ake zargi da aikata laifuka a Kano
Rundunar ‘yansandan jihar Kano tayi holin wadanda take zargi da aikata laifuka daban-daban daga ranar tara ga watan tara na shekarar 2020 zuwa Sha shida ga watan nan da muke ciki a yau juma’a.
A cewar rundunar ‘yan sandan ta Kano ta bakin mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa a wani taron manema labarai da rundunar ta gudanar da yammacin yau juma’a.
DSP Abdullahi Haruna ya kara da cewa cikin wadanda suka kama da aikata laifukan akwai masu garkuwa da mutane, fashi da makami, da dilolin kwayoyi tabar wiwi buhu-buhu da ‘yan yahu-yahu, ‘yan damfara da kuma masu bokanci na karya.
‘Yan sanda a Bauchi sun yi holen wasu mutane da ake zargin su da cin zarafin mata
Buhari ya sanya hannu kan dokar ‘yan sanda
Abdullahi Haruna Kiyawa ya kuma kara da cewa yanzu haka rundunar ta damu nasarar cafke masu satar wayoyin jama’a sama da mutane sittin da daya sakamakon cigaba da yawaitar samun satar wayoyi a fadin jihar Kano.
Wakilin mu na Kotu da ‘yan sanda Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito cewa rundunar tayi nasarar cafke wani matashi daya kware wajen satar baburan mutane wanda izuwa yanzu ya saci babura mai kafa biyu sama da guda dari biyar.
You must be logged in to post a comment Login