Labarai
‘Yan takarar shugabancin WTO za su bayyana gaban mambobin kungiyar
A cikin wannan makon ne ‘yan takarar neman zama babban daraktan kungiyar cinikin ta duniya, WTO su takwas daga nahiyoyin hudu na duniya za su bayyana gaban mambobin kungiyar don bayyana irin manufofin da suke da su kan ciyar da kungiyar gaba.
Bayan wuce matakin fitar da ‘yan takarar da aka kammala ranar 8 ga wannan wata na Yuli, ‘yan takarar, maza biyar da kuma mata uku, za su bayyana gaban mambobin kungiyar su 164 tun daga yau Laraba 15 ga wata zuwa jibi Juma’a 17 ga wata.
‘Yan takarar ,wadda daya daga cikin su ita ce tsohuwar ministar kudin Najeriya, Misis Ngozi Okonjo Iweala, wadda kuma Najeriyar ce ta tsayar da ita takarar zaben na neman karbar ragamar shugabancin kungiyar ne daga shugaban na yanzu, Roberto Azevedo da ke shirin ajiye mukamin nasa ranar 31 ga watan Agusta mai kamawa.
Sauran ‘yan takarar sun hada da Abdel-Hamid Mamdouh, dan kasar Masar da Amina Mohammed, ‘yar kasar Kenya da Jesus Kuri, dan Mixico da Tudor Ulianovschi, dan kasar Moldova da Yoo Myung-hee, dan kasar Korea da Mohammed Al-Tuwaijri dan kasar Saudi Arebiya da kuma Liam Fox dan kasar Birtaniya.
You must be logged in to post a comment Login