Manyan Labarai
Yansanda sun cafke wata mata da tura kishiyar ta rijiya a karamar hukumar Rano
Wata kishiya a garin Rurum mai suna Hauwa Lawan yar shekaru 30 ta tura yar’uwarta kishiya Zuwaira Sani cikin rijiya da goyon da mai suna Mustafa Sani dan shekara daya da rabi.
Yayin da rundunar Yansanda ta samu labarin ta kai dauki garin na Rururum inda suka tsamo ta zuwa asibiti daga nan ran Zuwaira Sani yayi halin sa.
Amma jaririn na ta dan shekara daya da rabi yana nan da rai.
A babban asibitin Rano ne dai Zuwaira Sani ta rasu.
Wacce ta aikata ta’asar Hauwa Lawan ta gudu
Mai maganin da yawun rundunar Yansanda ta Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan inda yace Kwamishinan yansanda na Jihar Kano CP Habu Sani ya bayar da umarnin a cafko Hauwwa duk inda take .
Da misalin karfe 1 da minti goma sha bakwai na dare ne Yansanda suka kamo Hauwa Lawan.
DSP Abdullahi Haruna yace kwamishinan yansanda na jihar Kano Habu Sani ya bayar da umarnin akai korafin babban sashin bincike na kisan kai dake rundunar yansanda dake Bompai domin fadada bincike.