Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu: An kuɓutar da wasu cikin ɗaliban kwalejin Kaduna daga masu garkuwa

Published

on

Biyar daga cikin dalibai 39 na kwalejin tarayya ta koyon ilimin tsirrai da gandun daji da masu garkuwa da mutane suka sace a Afaka sun shaki iskar ‘Yanci bayan shafe kwanaki 25 a hannunsu.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ne ya tabbatar da kubutar su ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin yau Litinin.

Aruwan ta cikin sanarwar ya ce, sojoji ne suka samu nasarar kubutar da daliban guda biyar daga hannun masu garkuwa da su da yammacin nan, bayan samun bayanan sirri na maboyar su.

A cewar sa, daliban yanzu haka suna sansanin sijoji don bincikar lafiyarsu, kafin a kai ga mika su zuwa iyalan su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!