Labarai
Yanzu-yanzu: An yi wani mummunan hatsarin mota a Kano
Ana fargabar wani hatsarin mota a Kwanar Dumawa da ke ƙaramar hukumar Minjibir a nan Kano ya haifar da asarar rayuka da jikkata mutane da dama.
Hatsarin ya faru ne da tsakar ranar Lahadi, inda wata babbar mota ƙirar DAF da ta taho daga birnin Kano ta faɗi.
Motar ta danne ƙaramar mota ƙirar Golf da kuma wata motar haya da ke lodi domin zuwa cikin garin Kano.
Sannan lamarin ya rutsa da wasu mutane da ke sana’a a bakin titi.
Labarai masu alaka:
Yadda aka sami asarar rayuka a hatsarin mota a Kano
Mutane 18 sun rasu sanadiyyar hatsarin kwale-kwale
Wani shaidar gani da ido mai suna Bashari Sule Dumawa ya shaida wa Freedom Radio cewa, sun miƙa mutane kusan 25 da lamarin ya rutsa da su zuwa asibitocin Minjibir dana Ɗanbatta.
Mun tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta ƙasa reshen jihar Kano Kabiru Ibrahim Daura wanda ya ce, kawo lokacin bai samu rahoton afkuwar lamarin ba, amma zai bincika.
Mun kuma ƙoƙarin ji daga mai magana da yawun ƴan sandan Kano amma bamu same shi a waya ba.
Shaidun gani da ido sun ce, an shafe sama da awa guda amma babu wasu jami’an bada agaji ko na tsaro da suka zo wurin.
Sai daga baya ne jami’an hukumar KAROTA suka kawo ɗauki, hakan ne ya sanya muka tuntuɓi mai magana da yawun hukumar Nabulisi Abubakar Ƙofar Na’isa.
Ya ce, sun je wurin domin kai ɗauki tare da kawar da motocin da hatsarin ya shafa.
You must be logged in to post a comment Login