Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu: Gwamna ya umarci a janye dokar hana zirga-zirga

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya umarci kwamishinan ƴan sanda da ya janye dokar hana zirga-zirga ta awanni 24 da aka sanya.

Gwamnan ya ce, janye dokar zai baiwa al’umma damar su fita su ci gaba da harkokin su kamar yadda suka saba.

Abba Kabir Yusuf ya baƙaci hakan da yammacin Alhamis ɗin nan ta bakin kwamishinan yaɗa labarai Baba Halilu Ɗantiye yayin zamam zartarwa.

Baba Halilu Ɗantiye ya ƙara da cewa kasancewar gobe juma’a da kuma irin halin da al’umma suke ciki na rashi, ya sa gwamnan ya bada wannan umarni domin a samar da sauƙi ga halin da ake ciki.

Sai dai gwamnan ya umarci al’umma da su kasance masu bin doka da oda domin wanzar da zaman lafiya a faɗin jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!