Sharhi
‘Yar Atiku Abubakar ta kama sana’ar sayar da abinci
Diyar tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ta baiwa al’ummar kasar nan mamaki,bayan bude gidan sai da abinci a birnin tarayya Abuja mai suna PIESTA RESTAURANT.
Walida wacce bata dade da kammala karatu ba a jami’ar Amurka dake birnin Yola na jihar Adamawa, ta baiwa al’ummar kasar nan mamaki matuka kasancewar ana musu kallon shafaffu da mai kuma ‘ya yan wanda suke da ido, ko rike da madafun iko da ka iya samun babban aiki a ma’aikatun gwamnatin tarayya.Mahaifin Walida, tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, da yake taya ta murnar bude wajen ya bayyana a shafin sa na Twitter kamar yadda kuke gani a kasa.
Congratulations to my daughter @walidaatiku and her team on the launch of @fiestameals. I am so proud of your entrepreneurial drive. You are a true illustration of @AUNigeria’s mission of training job creators. #VisitFiestaMeals https://t.co/KUwTmoyCmA
— Atiku Abubakar (@atiku) February 15, 2020
“ina alfahari da hazakarki ta kasuwanci. Kin kasance abin misali wajen koyar da matasa hanyoyin samar da ayyukan yi a kasa.”
Wannan dai na biyo bayan labarin da ya karade kasar nan na ‘yar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hanan wacce ta kama sana’ar daukar hoto jim kadan bayan ta kammala karatun ta na jami’a, a kasar Ingila.
A lokacin da dimbin matasan kasar nan ke neman gwamnati a dukkan matakai, data basu aiyyukan yi, sai gashi ‘ya yan masu hannu da shuni ko manyan mukarraban gwamnati da suka rike madafun iko a baya ko a yanzu, na kokarin gina ‘ya ‘yan su bisa tafarkin rungumar sana’o’in dogaro da kai ta harkar kasuwanci a fanni daban–daban.
Sai dai a bangare daya al’ummar kasar nan na ganin cewar masu abu ne da abun su wato Kura da kallabin kitse, suke yin kidan su tare da yi rawar su kasancewar suna da karfin dukiyar da zasu kama ko fara sana’a kowacce iri da taimakon iyayen su wanda talakawa da dama ba su da jarin da zasu fara ko da karamar sana’a ce.
Karanta:
Hanan Buhari: Sana’a Maganin zaman banza
Ina fatan Allah ya bani sana’ar da tafi Kannywood -Mansur Makeup
Lokaci ya yi da gwamnatoci a dukkan matakai za su fito da sabbin tsare-tsare da zai taimaka ko saukakawa miliyoyin matsan kasar nan da basu da ayyukan yi, don su kama sana’oi don dogaro da kansu.
Suma daga bangaren su matasan ya kamata ace sunyi karatun ta nutsu, da tunanin samar wa da kansu mafita don yin abinda zasu dogara da kansu ba tare da zaman jiran gwamnati ba, duba da cewar kasashe masu tasowa da wanda suka bunkasa, sana’o’i da ayyukan dogaro da kai na kan gaba wajen samawa matasa ayyukan yi ba hukumomi ba.
Idan har diyar Atiku Walida za ta kama sana’ar sai da abinci, a gefe daya Hanan Buhari ta yi daukar hoto, wane dalili ne zai hana talakan kasar samar wa da kansa mafita ta hanyar sana’a?
Yanzu dai za a iya cewa lokaci ya yi da za mu farka daga jiran ko ta kwana kasancewar kasar nan tana da dumbin al’ummar da zata samar da kasuwa ga duk sana’ar da aka dauka don dogaro da kai.
You must be logged in to post a comment Login