Addini
Yau mabiya addinin Kirista ke bikin Kirsimeti
Yau Jumu’a ashirin da biyar ga watan Disamba, rana ce da mabiya addinin Kirista a sassa daban-daban na duniya ke gudanar da bikin kirsimeti, domin murnar tunawa da ranar haihuwar Yesu Almasihu (Annabi Isah A.S).
A lokacin wannan biki, mabiya addinin Kirista kan gudanar da hidimomi na ibada cikin farin ciki.
A nan Najeriya ma gwamnatin tarayya ta bada hutu domin bikin wannan rana.
Freedom Radio ta halarci bikin a Cocin Ecwa bisharar Hausa da ke Kano.
Ga wasu cikin hotuna daga Cocin
A yayin bikin, mataimakin Fadan Cocin Rabaran Barau Isah ya ja hankalin al’umma kan su cire banbancin addini domin tabbatar da ci gaban Najeriya.
A cewarsa, jingine banbancin addini a tsakanin juna zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar ƙasar.
Rabaran Barau ya yi kira ga mabiya addinin Kirista da su yi biyayya da matakan kariya daga cutar Korona a yayin bukukuwan.
You must be logged in to post a comment Login