Kiwon Lafiya
Yawanci yara ‘yan arewacin kasar nan ne ke bata – RED CROSS
Kungiyar bayar da Agaji ta RED CROSS ta ce akalla mutane dubu 23 mafi yawancin su yara ne suka bata a Najeriya musamman a yankin arewacin kasar nan.
Ta cikin wani rahoto da kungiyar ta fitar ta bayyana cewa mafi yawan mutanen da suka batan, sun bata ne sakamakon rikicin Mayakan Boko Haram.
Sai dai kuma kungiyar ta RED CROSS ta bayyana takaicin ta kan yadda ta ce annobar Covid-19 na dakile aikin neman mutanen da suka batan da kuma hada su da iyalan su.
A cewar Rahoton, a Nahiyar Africa akalla mutane dubu 44 ne aka tabbatar da batun batan su sakamakon rikice-rikice da kuma sauyin yanayi da ke tilastawa jama’a yin gudun hijira.
Kungiyar ta kuma ce cikin wannan adadi kaso 45 yara ne, kuma kasashen Nigeria, Ethiophia, Sudan ta kudu, kamaru, Libya, Somalia, da jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ne ke da kaso 82 cikin dari na wadanda aka tabbatar da batan su.
You must be logged in to post a comment Login