Ƙetare
Za a bukaci fiye da Dala biliyan 3 don samar da agajin gaggawa a Sudan- MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, za a bukaci sama da Dala biliyan 3, domin samar da agajin gaggawa a Sudan mai fama da rikici yayin da ake fargabar sama da mutane miliyan daya za su tsere zuwa kasashen da ke makwabta da kasar a bana.
Haka kuma ta ce, a yanzu ana sa ran za a bukaci fiye da Dala biliyan 2, don samar da taimako ga Sudan din daga Dala biliyan 1 da aka kiyasta a karshen shekarar da ta gabata.
Yanzu haka dai an ci gaba da gwabza fada ne a kasar tun bayan ranar 15 ga Afrilu tsakanin babban hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar rundunar kai daukin gaggawa ta RSF.
Kimanin mutane 1,000 aka kashe, a ciki da wajen Khartoum babban birnin kasar da kuma yankin yammacin Darfur da ya samu hargitsewa a cewar likitoci.
Fiye da mutane 5,000 kuma sun jikkata, yayin da wasu miliyoyi ke ci gaba da zama a killace cikin gidajensu.
You must be logged in to post a comment Login