Kaduna
Za a fara aikin layin dogo daga Kano zuwa Abuja a watan Yuli – Amaechi

Ministan sufuri Rotomi Amechi ya ce, za a fara aikin layin dogo da ya tashi daga Kano zuwa Kaduna a watan gobe na Yuli.
Minsitan ya bayyana hakan ne a yau Juma’a yayin wata ziyarar duba aiki da ya kawo Kano.
Rotomi Amechi ya ce, inganta harkokin sufuri a fadin kasar nan zai taimaka wajen farfado da tattalin arziki.
A cewar ministan kula da hanyoyin sufuri zai taimakawa masu sanya hannayen jari kula da harkokinsu a fadin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login