Labarai
Za mu tallafawa makarantu da kayayyakin yaki da COVID -19 – Diamond Foundation
Gidauniyar tallafawa Marayu da gajiyayyu wato Diamond Foundation for less privileges and orphans ta nanata kudirinta na cigaba da samar da kayayyakin yaki da annobar cutar Covid-19 ga daliban makarantu a daidai lokacin da aka dawo cigaba da karatu a fadin Jihar Kano.
Shugaban Gidauniyar Usman Ibrahim wanda aka fi sani da suna Diamond ne ya bayyana hakan a yau lokacin da gidauniyar ke kaddamar da rabon kayayyakin kariya daga annobar cutar Corona a makarantar Primary ta Unguwar Tukuntawa Kano.
Usman Diamond ya kara da cewa la’akari da irin yadda gwamnatin Kano ke kokari wajen yaki da cutar Covid-19 ya sanya shi daukar matakin bada tasa gudunmawar kasancewar abun yayi wa gwamnatin Kano yawa domin rage mata nauyi.
Malam Auwal Ilyasu shine Shugaban Makarantar Primary ta Tukuntawa ya bayyana jin dadinsa tare da kira ga gwamnati data samarwa makarantar abun zama domin akwai dalibai sama da dubu daya da dari takwas da hamsin amma a kasa suke zama shekaru biyu kenan.
COVID- 19 : CBN ta rarraba tsabar kudi Naira biliyan 69
Yaƙi da rashawa: Muhyi ya fara raba kayan tallafin Corona da ya ƙwato
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito cewa cikin kayayyakin da gidauniyar ta rabawa daliban akwai Takunkumin rufe fuska guda dari da kuma botikin tara ruwa don wanke hannu sai kuma sinadarin wanke hannu wato Handsanitizer.
You must be logged in to post a comment Login