Labarai
Za mu zakulo matasa masu basira don basu gurbin karatu a Maryam Abacha – Dakta Bala
Daga: Hajara Hassan Sulaiman
Jami’ar Maryam Abacha da ke Maradi a jamhuriyar Nijer ta ce za ta mayar da hankali wajen zakulo yaran da suke da fasaha kuma basu da damar shiga makaranta don ba su tallafin yin karatu.
Daraktan kulla alaka da hadin guiwar na kasa da kasa a jami’ar Maryam Abacha Dakta Bala Muhammad Tukur ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan tashar Freddom Redio.
Dakta Bala Muhammad ya kuma ce, a yanzu jami’ar ta samar da cibiya anan Kano don saukakawa dalibai ketarawa zuwa sassa daban-daban na duniya don neman ilimi.
Ya ce, “wannan ya sanya a yanzu da aka samar da cibiyar makarantar anan Kano za mu binciki masu unguwanni da dagatai har ma da hakimai da amsu unguwanni don su bamu rahoton yaron da yake da basira don mu bashi gurbin karatu a jami’ar”
You must be logged in to post a comment Login