Labarai
Za’a bude makarantu a jihar Katsina
Gwamnatin jihar Katsina ta ayyana ranar 5 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za’a bude makarantun sakandire da na firimare masu zaman kansu da na gwamnati a fadin jihar.
Kwamishinan ilimi na jihar Badamasi Lawal ne ya bayyana haka, a wata hira da manema labarai, inda ya ce za a fara bitar darussan zango na biyu da zarar an makarantun.
Ya kuma ce, bayan an kammala bitar karatun sai kuma a fara gudanar da jarabawar karshen zangon na biya a ranar 19 zuwa 23 na watan na Oktoba.
“Daliban za su dawo makaranta don ci gaba da zango na uku wanda za a fara a ranar 26 ga watan Oktoba zuwa ranar 24 ga watan Janairun shekarar 2021, sai a gudanar da jarabawa daga ranar 25 ga watan Janairun a kuma kammala ranar 5 ga watan Faburairu.” In ji shi.
Ya ce ya zama wajibi dalibai da kuma malamai su yi amfani da takunkumin rufe fuska tare da kiyaye ka’idojin bada tazara domin kariya daga cutar Corona.
You must be logged in to post a comment Login