Labarai
Za’a bude makarantu nan gaba kadan – Sani Aliyu
Gwamnatin tarayya ta fara shirye-shiryen bada Umarnin bude makarantu a fadin kasar bayan shafe Tsawon lokaci a kulle sakamkon Annobar cutar Covid 19
Shugaban kula da shirin yaki da Cutar Covid 19 Dr. Sani Aliyu ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a filin jirgin saman Nnamdi Azikew dake Abuja.
Dakta Sani Aliyu ya kara dacewa bude makarantun zai kasance karkarshin kwamitin kulawa na musamman a wani bangare na kare daliban daga cutar ta Corona.
A cewar sa makarantun da za’a bude sun hadar da makartun firamare da sakandire da kuma kwalejojijin ilimi.
Dakta Sani Aliyu ya ce ya zama wajibi gwamntocin jahohi su kafa kwamitin da zai rika kula da hallun da makaruntu ke ciki don kariya daga cutar ta Corona.
You must be logged in to post a comment Login