Labaran Kano
Za’a dawo da ma’aikatun casar Shinkafa a Kano -Nanono
Gwamnatin tarayya ta sha alwashin farfado da kuma inganta ma’aikatun casar shinkafa 17 dake nan jihar Kano, tare da samar da sabon tsarin aikin noma na zamani a jihohin Kano da Bauchi nan ba da dadewa ba.
Ministan noma Alhaji Sabo Na Nono, ne ya bayyana haka a yau, a wani taron masu ruwa da tsaki a harkokin Noma da ya gudana tsakanin sa da manoma a dakin taro na Coronation Hall, dake fadar gwamnatin jihar Kano, don samar da ingantaccen tsarin aikin noma na zamani tare da Samar da wadataccen abinci a kasa baki daya.
Alhaji Sabo Na Nono, yace tsohon tsarin da ake amfani dashi na Noma yana cike da kalubale kasancewar a kididdigga kasar nan tana da manoma miliyan 70, amma kwararrun masana na noman zamani da ake dasu a fannin na noma dubu goma 14 ne daga cikin Miliyoyin manoma.
Don haka gwamnatin tarayya zata fito da shirye -shirye a fadin kasa gaba daya a kananan hukumomi 632, wanda za’a samar da cibiyoyin bunkasawa da sarrafawa wato (Service centres) ga manoman kasar nan.
A nasu bangaren, manoma da suka halarci taron, ta bakin Alhaji Mukhtari Saleh da Mustapha Halilu sun bayyana babban kalubalen da ake fuskanta a tsarin noma, wanda matukar gwamnatin bata samar da gyara ba ko mafita za ayi ta samu koma baya a bangaren Noma a kasar nan ,musamman ga kananan manoma.
Wakilin mu Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito mana cewa dumbin manoma, da kungiyoyin su ne suka halarci taron a yau tare da gabatar da bayanai, da tambayoyi ga ministan noman don samar da kyaykyawar hanyar inganta Noma a kasar nan tun daga tushe tare da zamanan tar dashi.
RUBUTU MASU ALAKA:
Za’a fadada gidan abincin N30 zuwa kananan hukumomi 44 na Kano
Shugaban kasa ya damka Amanar biliyan 183 a hannun Kanawa
Shugaban kasa ya damka Amanar biliyan 183 a hannun Kanawa