Labarai
Za’a fara rataye masu garkuwa da mutane a Katsina
Rundunar ‘yansadan ta jihar Katsina, ta ce za fara rataye masu garkuwa da mutane nan ba dadewa ba.
Kakakin rundunar ‘yansandan ta jihar Katsina, SP Gambo Isah ne ya bayyana haka a wata takarda da ya sakawa hannu aka rabawa manema labarai.
Takardar ta kara da cewa, ta bankado wani makarci da wasu batagari, ke amfani dashi ta hanyar kiran al’umma ko tura sakon kar ta kwana da cewar an yi garkuwa da ‘yan uwansu tare da yin kira gare su da su hanzarta biyan wasu makudan kudade ko a yi garkuwa dasu ko wasu daga cikin dangin su.
An kashe barayin shanu da masu garkuwa da mutane a Katsina
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama masu garkuwa da mutane 93
Don haka rundunar take gargadi da kakkausar murya ga masu aikata hakan cewa doka zatayi aiki a kansu kamar yadda ta tanada.
Hukumar ‘yansandan tace al’umma su sani cewa sashen doka na jihar Katsina, ta garkuwa da mutane wacce akayi wa kwaskwarima sashe na dari biyu da arba’in da uku, ya tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk mai aikata garkuwa da mutane.
Hukumar ta kuma umarci iyaye da su saka ido a yankunan su da zirga zirga ta bakin fuskoki ko abinda basu aminta dashi ba kasancewar doka zata yi aiki akan duk wanda aka samu da laifi ba sa ni ba sabo.
You must be logged in to post a comment Login