Addini
Naɗin Muhammadu Sanusi a matsayin Khalifan Tijjaniya alheri ne ga Najeriya – Jagororin Tijjaniya

Wasu daga cikin manƴan shehunan ɗarikar Tijjaniya sun bayyana zabar sarkin Kano na goma sha huɗu a daular fulani Malam Muhammadu Sanusi na 2 a matsayin khalifan ɗarikar Tijjaniya a Najeriya da cewa alheri ne ga kasar.
Shehunan ɗarikar Tijjaniyar sun bayyana hakan ne yayin wata ziyarar mubaya’a da suka kai wa tsohon gwamnan babban bankin na Najeriya a gidan sa da ke Kaduna.
A cewar su kafatanin mabiya ɗarikar Tijjaniya a duniya suna alfahari da nadin Malam Muhammadu Sanusi na biyu a matsayin shugaban ɗarikar Tijjaniya a Najeriya
Ziyarar wadda wakilan shugaban ɗarikar ta duniya Sheikh Abdul-Ahad Nyass suka kai masa sun ce sarkin na Kano na goma sha hudu a daular fulani mutum ne na gari da ya dace da jagorancin Tijjaniya.
You must be logged in to post a comment Login