Coronavirus
Zamfara ta karbi kason farko na allurar rigakafin corona
Gwamnatin jihar Zamfara ta karbi kason farko na allurar rigakafin cutar ta COVID-19 wanda yawansu yakai dubu 55,000 don yiwa kimanin mutane dubu 27,000.
Kwamishinan lafiya na jihar Alhaji Yahaya Muhammad Kanoma ne ya bayyana hakan ga manema labarai lokacin da yake karbar alluran rigakafin.
Kanoma ya ce allurar rigakafin za ta isa a yiwa mutane dubu 27,000 har zagaye biyu.
Ya kuma ce za a fara yiwa ma’aikatan gwamnati, malamai, ‘yan jarida, direbobin motocin haya da sauran su.
A cewar Kanoma tuni gwamnatin jihar ta horar da wasu ma’aikatan da za su kula da aikin allurar duk da cewa jihar Zamfara itace ke da mafi karancin masu dauke da cutar corona a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login