Rahotonni
Zamu hukunta duk basaraken da ya fita daga Zamfara – Matawalle
Gwamnatin jihar Zamfara ta haramta wa shuwagabannin al’umma fita daga yankunan su har tsawon wata uku.
Wadanda aka haramtawa fitar sun hadar da sarakunan jihar goma sha bakwai da shugabannin rikon kananan hukumomin jihar.
Gwamnan jihar, Muhammad Matawalle ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da Freedom Radio.
Gwamnan ya ce, an cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da malaman addini da masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro.
Labarai masu alaka
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta amince da sabuwar dokar ma’adanai
Na fara sayen Zinare don magance matsalar tsaro – Gwamnan Zamfara
A cewar sa, dama mutanen jihar sun dade suna basu makamanciyar wannan shawara, a don haka aka dauki wannan mataki.
Matawalle yace wannan abu ne mai kyau, kasancewar ko da wani abu zai faru to za a tuntubi gwamnati da jami’an tsaro cikin hanzari.
Haka kuma ya ce, ya basu wa’adin watanni uku don ganin an sami saukin al’amuran tsaro a jihar.
Gwamnan ya kuma ce duk sarki ko shugaban karamar hukumar da aka sami matsalar ‘yan ta’adda a jihar sa, kuma baya nan to ya zama wajibi gwamnati ta hukunta shi.
You must be logged in to post a comment Login