Kiwon Lafiya
Zulum zai dauki ma’aikatan lafiya aiki a Borno
Gwamnatin Jihar Borno za ta dauke ma’aikatan lafiya aikin yi guda dari shida da saba’in da nufin kara inganta Asibitocin da ke fadin Jihar.
Gwamnan Jihar Babagana Zulum ne ya bayyana hakan a wani taro da masu ruwa da tsaki na bangaren lafiya da ya gudana a birnin Maiduguri, Jihar Borno.
A cewar Zulum, za a dauke sabbin ma’iakatan Jinya su tamanin da hudu sai kuma Likitoci da ungozomomi dari uku da sittin da biyar, da masu hada magunguna da mataimakasu dari biyar da tamanin da hudu.
Zulum yana mai cewa, daukan sabbin ma’aikatan jinya zai kara wa bangaren lafiya Jihar karsashi wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata baya kula da marasa lafiya sosai.
Daga cikin wadanda suka hallarci tattaunawar akwai kwamishinan lafiya na Jihar DR Salihu Kwayabura da shugaban hukumar ungozomomi Umar Shettima da dai sauransu.
You must be logged in to post a comment Login