Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan siyasa ne suka taɓarɓare Najeriya – Rochas Okorocha

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Imo kuma sanata a majalisar dattawan Najeriya, Rochas Okorocha, ya zargi yan siyasar ƙasar nan da hannu wajen taɓarɓarewar al’amuran ta.

Sanata Rochas ya ce rashin bai wa masu kishin kasa damar mulkar ƙasar nan, na daga cikin dalilan da suka sanya ake samun ƙaruwar masu neman a raba ƙasar.

Sanatan ya bayyana hakan ne, a yayin tattaunawarsa da BBC Hausa anan Kano, inda ya ce idan har ‘yan siyasa suka yadda da za su samar da haɗin kai a tsakanin jama’a, to kuwa za a cimma manufa.

Rochas ya kuma ce, abu ne mai wahala a samu warwarewar matsalar, matukar yan siyasa ba su cire son kan su ba, tare da sanya buƙatar al’umma a gaba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!